labaran duniya

Yammata dake son su zama governor a kano

Wani abin mamaki da ba a taba ganin irinsa ba, mata da yawa sun fito takarar gwamna a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Kano dai na daya daga cikin manyan jihohin arewacin Najeriya, kuma jiha ce wacce ta yi kaurin suna wajen tatagurzar siyasa.

A tarihin jihar dai mace bata taba rike wani mukami na shugabanci ba a matakin gwamna.

Matan bakwai sun fito ne a jam’iyyu daban-daban, kuma kowacce na da manufofinta na musamman ga al’ummar Kano idan ta lashe zaben. 

Fauziyya Kabir Tukur ta zauna da hudu daga cikin wadannan matan ga kuma karin bayani a kan su. 

Safiyya Salisu Abdul

 • Jam’iyya: National Unity Party (NUP)
 • Shekaru: 40
 • Karamar Hukuma: Dala Ward, unguwar Yalwa
 • Manufarta: “Idan aka zabe ni a matsayin gwamna a jihar Kano, zan tabbatar da tsaro ga al’ummata kuma zan dauki kyakkyawan mataki wajen ganin jihata ta yi zarra.”

Maimuna Muhammad 

 • Jam’iyya: United Progressive Party (UPP)
 • Shekaru: 40 
 • Karamar Hukuma: Kano Municipal, unguwar Indabawa
 • Manufarta: “Na yi aikin sa kai a asibitoci, kuma na ga halin da mutanenmu ke ciki. Don haka na dau niyyar kawo ci gaba mai yawa a fannin ilimi da lafiya da samarwa matasa ayyukan yi.”

Halima M Ahmad 

 • Jam’iyya: Alliance for Democracy (AD)
 • Shekaru: 55
 • Karamar Hukuma: Gwale
 • Manufarta: “Idan na samu nasarar zama gwamna a jihar kano, zan tabbatar da cewa na yi aiki tukuru wajen ganin cewa al’ummar jihar sun samu martaba a kasarmu.”

Sauran ‘yan takarar sun hada da Fatima Danladi Musa ta jam’iyyar RPN (Restoration Party of Nigeria), da Rukayya M Abdullahi ta jam’iyyar DPC (Democratic Peoples Congress) da Umma Ibrahim Adhama ta jam’iyyar CAP (Change Advocacy Party) da Furera Ahmad ta jam’iyyar FDP (Fresh Democratic party) da kuma Amina Yusuf ta jam’iyyar NAC (National Action Congress). 

Wadannan matan dai suna ganin akwai sauyin da za su iya kawo wa ga al’umma idan suka yi nasara, sai dai daga jin ta bakin mutane da BBC ta yi a Kano din, ga alama ba su yi farin jini ba, ko kuma farin jinin nasu bai taka kara ya karya ba. 

Leave a Reply

Theme by Anders Norén