labaran duniya, Sanarwa, Wakokin siyasa

Matakan zaben najeriya na 2019 guda bakwai

Hukumar Zaben Najeriya INEC ta fitar da wasu sabbin matakai bakwai da mai zabe zai bi kafin ya jefa kuri’a, a ranar zaben gabanin manyan zabukan kasar da za a yi a watan gobe.

Hukumar ta sanar da wadannan matakan ne a shafinta na Twitter a yayin da gwamnatin Jamus ta yi kira gare ta da ta tabbatar ta kwatanta gaskiya da adalci wajen gudanar da zabukan.

Kakakin hukumar Malam Aliyu Bello ya bayyana wa BBC cewa hukumar zaben ta fitar da wadannan matakan ne don wayar da kan mutane kan matakan yin zabe.

Matakin farko shi ne na tantancewa, inda wani jami’in hukumar zai tantance “mai kada kuri’a kuma ya tabbatar da cewa a rumfar mai kada kuri’ar yake,” in ji shi.

Mataki na gaba shi ne inda wani jami’in INEC zai duba katin zaben mai kada kuri’a a kan na’urar ‘Card Reader’ kuma ya tabbatar cewa katin nasa ne.

A mataki na uku ne “ma’aikacin INEC zai duba sunan mai kada kuri’a a jerin sunayen masu kada kuri’a, sannan a sa masa alama a jikin yatsansa don nuna cewa an tantace shi.”

Daga nan sai mataki na hudu inda wani jami’in hukumar INEC din daban zai bai wa mai kada kuri’a takardar jefa kuri’ar.

A mataki na biyar kuwa shi ne inda mai kada kuri’a zai zabi jam’iyyar da yake so cikin sirri, kuma ya nade takardar sannan ya jefa ta a cikin akwati.

Mataki na shida shi ne da zarar mai zabe ya jefa takardar, ya kammala zabensa, kamar yadda kakakin hukumar ya ce.

Mataki na bakwai kuma shi ne inda mai kada kuri’a yake da zabin ko ya tsaya sai an kammala kidaya kuri’u ko kuma ya tafi.

Har ila yau Malam Aliyu Bello ya ce yana ganin wannan tsari da INEC ta fitar zai saukaka tsarin kada kuri’a.

Ya ce a baya, mutane da yawa ba su da masaniyar hanyoyin da ake bi a jefa kuri’a kuma hakan kan janyo tsaiko a rumfunan zabe.

Leave a Reply

Theme by Anders Norén