FASSARAR AREWA24

Gidan badamasi Episode 1 latest hausa series

DOWNLOAD HERE

Gidan Badamasi sabon wasan kwaikwayon (film) din barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji mai suna Alhaji Badamasi. Badamasi dattijon attajiri Mai shekaru 70 yayi aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi ‘ya’ya masu yawan gaske, wasu ma bai San Ina suke ba a halin yanzu. A cikin wasan kwaikwayon an fara Kai ruwa rana ne a lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cikawa ‘ya’yansa alkawarin kudin da ya yi musu. Yaki ya barke tsakanin marowacin uba da handamammu/kwadayayyun ‘ya’yansa. Gidan Badamasi Fim ne na barkwanci mai dauke da ilmantarwa, fadakarwa da nishadantarwa ta hanyar amfani da gwanayen kuma zakakuran ‘yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai saka idanu yana jiran ganin abin da zai wakana a nan gaba. Gidan Badamasi. Sabon shirin zai dinga zuwa muku duk ranar Alhamis (Thursday) da misalin karfe 8:00 na dare, sannan a maimaita shirin ranar Lahadi (Sunday) 9:00 na safe a tashar #arewa24channel. Shirin: Nazir Adam Salih Daukar hoto: Nelcon Nel

Leave a Reply

Theme by Anders Norén