Sanarwa

Yan Damfara Episode 2 sirrin dabaru

Sirrin dabarun yan damfara Episode 2

Kuyi hattara masu son banzar katin waya da data… wannan Sakon nada matukar mahimmanci ga al’umma wallahi

Da farko ka karanta abin dake cikin wannan hoton zanyi ma bayani dalla dalla domin yan damfara ne suke yaudarar mutane

1-wannan dandamfara yayi kokarin nunawa bashi ya shigo Da wannan tsarin ba, yace “kwanaki wani yayi posting din wannan abun, yana ganin shima kamar karyane, amma sai yasamu biro ya rubuta a takadda ya gwada, ya rantse yace yaga Da gaskene yanzu haka wai dashi yake amfani hhh”

2-“yace yanada 21360 a account dinsa na mtn shiyasa yake yadashi a gari domin kowa yaga abin mamaki”

3-ya kara nunawa mutane cewa bashi yayi wannan posting din ba inda yake cewa “ga abin da suka rubuta kamar haka”mtn sun kara rikicewa a kwanakinnan ga sirrin cin banza da zai bayar ta katin mtn wacce mutum zai tara kudi Da mb yadda yakeso hh” kaji fa wai yadda mutum yake so,

4- yace “in hardai layin mtn ne dakai to I dan kasa zasu baka “

5-yace “”1-katin 200 dubu 500 tare Da 2gb

“2-katin 400 dubu 15000 tare Da 4gb

3-Katin 750 dubu 25000 tare Da 7.5gb””

6-sannan ya nunawa mutane cewa akwai sharadi domin mutane su kara yarda cewa Da gaske yake in da yake cewa “akwai sharadi kada ayi amfani Da katin 1500 hhh wai domin bayayi”hm

7-sannan yace ga matakan da zaku bi “ (1) yanaso mutum yabar kamar naira 5 ko 10 a layin wayarsa in ba haka ba message din bazai zoba. (2) yace mutum ya siyo katin 200 ko 400 ko 750. (3) sai mutum yaje wajan message na wayarsa ya *serial number* ma’ana *lambobin katin* wai sai mutum yasa

[ *lambar katin pin*131*lmdf# ]

Wai sai mutum ya tura zuwa wannan code din na mtn, hhh (0092348105106453)

8-sannnan yace “bayan ka tura sai ka dan jira kadan Sakonni ta wayar sai shigo kamar haka

Your lmdf is… misali 1234 wai Da Zarar message din ya shigo sai kasa katin a wayarka kasa *555*lambar katin*lmdf Da aka turoma ta message#. Hhh wai nan take zaka sha mamaki harda rantsuwa wai zakaga 200-5000 Da 2gb ko 400-15000 Da 4gb ko 750-25000 Da 7.5gb hhh

9-sannan yace a gaggauta sawa don kar abar mutane a baya kar mtn su gano su toshe hanyar

10-your awu4fu airtime is valid for 30 days

Abinda labarin ya kunsa a takaice shine

Danfara yayi tsarinne ta inda zaisa mutane su tura masa katin waya na mtn bayan mutum ya tura masa lambobin katin shikuma zaisa a wayarsa kafin kasa, idan yasa katin a wayarsa ko kasa katin kamar yadda yace a karshe katin bazai shiga ba…

Ga dabaran Da yayi amfani dasu

1-ya kirkiri wani Abu na banza wai [lmdf]

2-yayi amfani Da wannan code din (0092348105106453) wanda mutane basu san cewa lambar wayar sa bace

Ga yadda ya hada code din= kowacce kasa tana Da code din da take amfani dashi wajan layikan waya, wanda idan mutum yana wata kasar yanaso ya kirawo lambar mutum ta wani

Kasar sai yasa code din zata shiga, code din nigeria shine [ 234 ] ma’ana idan kana kasar waje zaka kirawo dan nigeria sai ka kara wadannan lambobin 234 a farkon lambarsa misali- 23408023456789 zaka iya cire 0 din farko ta lambar ka fara sawa kamar haka 2348023456789 sannan zaka iya sa ko lamba nawace a farkon lambar indai kasa 234 kafin farkon lambar to zata shiga misali kamar yadda wannan Dan damfara yasa a lambarsa

(Ya kara 009 sannan yasa 234 ya cire 0 farko yasa 8105106453 I Dan ka hada lambar zai baka [0092348105106453] kaga wannan code din ya tashi a matsayin lambar wayarsa ta mtn wacce za’a tura mai katin

3-kaga ya kautar Da hankalin jama’a wajan canja lambarsa amai makon yasa 08105164…

Yasa 0092348105164… don mutane su dauka code din mtn ne, wanda abin ba haka yake ba

Wannan abin idan mutum bashi da Sani akan wannan abubuwan to lalle za ayi nasara akansa

Harinsa akan talakawa yake Da alama

Don da 200 dinnan zai samu kudi makudai masu tarin yawa misali kasa 200 sau 1000 zaka ga ya baka 200000 wanda baasan mutum nawa ne zasu fada wannan tarkon ba

Don allah katurawa mutane wannnan Sakon domin su kaucewa wannan tarkon

Sannan zaku iya turo mana wasu bayanan kan yan damfara wanda suka damfari wani wanda ka sani ka gaya mana yadda suka damfare shi domin fadakar Da al’umma

Gmail= arewanishadi@gmail.com

Ko ka rubuto mana a comment a kasan wannan bayani

Mungode Da lokacin ku

Sako daga www.arewanishadi.com

6 Comments

  1. Natsakiya

    Da kyau

  2. Bunu

    Assalamualekum dear friend don Allah kuna samana irin Chinese hausa action films dakuma irin finafinanda na Indiawa nafassarar Hausa

Leave a Reply

Theme by Anders Norén