Sanarwa

Yan Damfara episode 1 sirrin dabaru

Sirrin dabarun yan damfara Episode 1

Karanta domin kaucewa yan damfara na zamani

Yan damfara sun bullo Da wata sabuwar hanya ta damfarar mutane a yanar Gizo

Wanda mutane Da yawa na tabbata zasu fada tarkon su,

Kamar dai yadda kuka Sani San banza shike janyowa mutane Asara ako da yaushe

Yan damfara sukan bawa mutane kudi maiyawa ba tare Da sun damu ba, hakan zaisa idan suka bawa mutum shi kuma zai saki jiki dasu, su kuma su damfare shi

Kaso 90 na bincike ya nuna Akan damfari mutum ne ta hanyar son banza

Misali za’a kawo ma Abu ana siyar dashi dubu dari 100,000 ace ka bada dubu arba’in musamman in kasuwanci kake zaka bukaci abubuwan Da yawa zasu fara baka abubuwan kyautama ko bashi domin ka yarda dasu sosai,

Wasu yan damfaran zasu iya daukar tsawon lokaci kafin su damfare ka sai sun gama kashe ma kudi sannan akarshe su bukaci ka tura musu Da kudi zasu kawo ma kaya anyi order zasu gayama kudin kayan a matukar sauki,

Dama kai ka yadda dasu sai ka tura musu kudin, daga karshe ka nemesu ka rasa

Wadannan mutane na Da matukar hatsarin gaske, wasu suna ganin kamar tsafi suke, wanda abin ba haka yake ba, tsananin basira ne da tunani suke amfani dashi wajan nasara akan wanda suke hari,

Duk Dabarar mutum wallahi zasu iya nasara akansa, addu’a ce kadai zata taimakeka ba zasuyi nasara akan ka ba

Makasudin wannan labarin shine mu gujewa Abu guda uku kamar haka,

1-son banza akan kayan kasuwanci ko wani abun more rayuwa

2-saurin yadda Da abokin kasuwancin Da bakasan asalin sa ba

3-turawa mutum kudi ta internet ba tare Da kasan mutum ba ko kaga kayan ya aiko ma ba

Wadannan abubuwa guda uku zasu taimakeka wajan kaucewa yan damfara ako wanne Hali, sannan ka yawaita addu’a Da sadaka insha allah allah zai kareka daga sharrin su

Bincike ya nuna ana matukar damfarar mutane Da wadannan abubuwa sosai Da sosai musamman a yankin africa

Don allah mukula sosai mu gujewa son banza…

Ka turawa mutane wannan bayanin domin suma su ankarta…

Mun gode Da lokacin ku daga

Www.arewanishadi.com

Leave a Reply

Theme by Anders Norén