Da Sauran rina

Da Sauran Rina 2 Episode 7 A RUBUCE littafin hausa

A Episode 6 mun tsaya a inda ake cewa

“Ai buhaila in ba Zahraddini ta aura ba ban San wace irin Damuwa zata shiga ba”

Ihsan ta ce. “Kai ke dai da surutu ki ke, ma ta gaya miki hakan?” Abdallah ya nufi dakinsu, Buhailan tana ce bisa gado ta lullube da bargon ya taba ta ya ji zafi rau ta bude idanunta suka hada kwance ido ta juya ta tsani ganinsa saboda tana son Zahraddin ya kama hannunta ya mikar da ita zaune, ya ce, “Buhaila har Zahraddin yana da matsayin da za ki tsani ‘yan uwansa a kansa?” Ta yi rau-rau da ido ba ta ce komai ba, ya ce. “Shi ke nan ki ba ni lambar wayar Zahraddin din zan kira in ba shi hakuri ya zo ki aure shi a yau ma Karewar soyayya tunda kina ganin na yi miki ba daidai ba, amma ina so ki sani daga yau ba zan Kara shiga sha’aninki da samarinki ba” Ya juya zai fita, ta riko hannunsa, ta ce. “Don Allah ka yi hakuri Yaya”. Ya ce, “Ke za a ba hakuri”. Ta ce, “Ba haka ba ne” Ya ce, “Haka ne mana tunda har ga shi ciwo ya kama ki don damuwa?” Ya fice ya barta a gurin.

Falon Abba ya shiga, shi kadai ne yana jan carbi har yanzu akwai yanayin da a tare da Abban ya zauna suka gaisa.Abba yace Abdallah na gama maka shirin tafiya Malaysia na tanadi hotunan yammata guda uku ‘ya’yan abokaina ne za k tafi da su ka gaya masa na ce lallai a cikinsu ya zabi daya matuKar yana son ci gaba da zama lafiya da ni, na ba shi wata biyu duk abin da yake ciki ya tattara ya baro Malaysia ya dawo gida, da ma wadannan shekaru biyun da ya Kara wa kansa ina zargin akwai dalilin da ya sa ya dage sai ya Kara, ko ya gama karatunsa ko bai gama ka gaya masa ya dawo yanzu kam kafin ya dawo za a daura masa aure, zai iske matarsa… Abdallah ya zuba wa hotunan ido, tausayin Najib ya kama shi, zai yi magana Abba ya ce “Ya isa ba na son surutu, ka yi abin da na gaya maka kawai Lokacin da Mama ta ji labarin tafiyar Abdallah Malaysia murmushi ta yi ta ce da Mami, “Ai na gaya miki akwai gagarumin abin da su Abba suka gani a Malaysia tare da Najib, idan kin lura za ki ga gabadayansu suna da

damuwa, tunda suka dawo daga Malaysian nan abba bai cin abincin kirki, ba ya bacci ga shi an ce yau din nan Abdallah zai Kara komawa. Idan ba rami ba abin da ke kawo batun rami” Mami ta ce, “Ai ni tun a daren jikya na kira Najib din a waya ban ji wata damuwa a tare da shi ba. Mun yi hira lafiya Kalau” Ta ce, “Ko ma dai mene ne za mu ji ne” Hankalin Abdallah a tashe yake don a zahiri Buhaila a cikin damuwa ta ke, bai san ta yadda zai bayyana mata damuwarsa game da ita ba, ballantana ya nemi soyayyarta da hadin kanta, har ga shi hankalinta ya tattara kan soyayyar wani, da gaske kuma ta ke son Zahraddin, daidai lokacin da soyayyarta ke Kara daga masa hankali da tunani ga tafiya ta same shi wadda ta zamo masa dole. Da yammma zai tafi har suka fita suka dawo da la’asar ba shi da kuzari, ya yi wanka ya tsuke cikin Kananan kaya ya fito zuwa cikin gida. ya yi sallama da su Mama, Buhaila na kwance kan kujera idanunta rufe ta bude ita ma ta yi masa fatan dawowa lafiya. Yana matuKar son kebewa ya yi magana da ita, ya rasa yadda zai yi, ya fahinci mutanen

gidan sun fara yi masa wani irin kallo a akan buhaila, gabadaya harsu fati Da ihsan hanawa zance, amma dai ya fi zafafawa kan Buhaila, amma wasu suna ganin don ta fi rawar kai ne, Fati ke bin bayanta, Ihsan kuwa tunda suka yi candy ba ta taba zance da wani a Kofar gidansu ba, halayyarta daban ce, in ban da tana da masifar jin kai da sai a ce ta fi su, miskilancinta da isa ke hada ta da mutane. Lokacin da ya shiga mota ya zauna yayi tagumi yana tunanin rashin cancantar boye wa Buhaila sirrin zuciyarsa da yake, wannan kuskure ne babba. Tafiya ce ta same shi a yau ba da shirinsa ba, a wannan ranar ce ya yi niyyar bayyana mata cewa, yana sonta duk abin da zai faru ya faru. Direban da zai kai shi airport ya tada mota kamar zai ce ya tsaya ya bayyana mata soyayyarsa, sai kuma ya yi shiru su;ka tafi. Abdallah na kashingide kan kujera yana shan lemo, Najib na zaune daf da shi a Kasa ya yi tagumi da hannaye biyu yana kallon hotunan yammatan da Abdallah ya kawo masa wadanda

Suke ajiye a kan cinyarsa, da kyar yake iya fidda numfashi, ya gaji ya watsar da hotunan ya mike zai fita. Abdallah lya mike shi ma ya ce. “Yadda ka watsar da wadannan hotunan haka ka watsar da batun Abba, abin da zan koma in gaya masa ke nan’ Najib ya koma ya zauna ya ce. Ni ban ce maka na watsar da maganar Abba ba, taka maganar na watsar don n tabbatar kai ne ka Kulla wannan shawarar, me zan yi da wadannan ‘yammatan ko da a ce idanuna ba su bude da mace ba?” Abdallah bai yi niyyar dariya ba, amma sai da ya kyalkyale da dariya, ya ce. “Ka ji ihu bayan hari, to ni ina ruwana? Ni fa aiko ni aka yi. ka ga da zabinka da rashin zabinka duk daya za a daura maka aure Najib!” Bacin ai ya sa Najib ya ce “Zaman Kasar nan ne ba kwa son in ci gaba da yi, zan tafi gida tare da kai, amma ha zan auri matar da ba na so ba a cikin hotunan nan ba wadda ta yi min” Abdallah ya tabe baki ya ce “Wannan ya rage yá nak a Najib

Ya bar Abdallah a falon ya fita zuwa inda ya san zai iske Mainasara yana nan kuwa tare da sabuwar yarinyarsa Zeezee suna matsar junansu kamar cingam haka suke manne wa juna. Najib ya harari Zee ya ce. “Ke dai ko mayya sai haka, ke ce ki ke sa Mainasara yana ramewa kullum abu daya ba hutawa Da jin haka sai Zee ta janye jikinta daga “Kai dan bakin ciki ne Najib, duk abinka Ya yi murmushi ya ce. Mainasara tana bambami ta ce ba ka isa ka raba ni da Mainasara ba”. “Ni ma ban ce zan raba ku ba Zec, so nake dai ki dinga dan jan ajinki irin na mata, kullum kina manne da namiji Ta ja tsaki ta shige bandaki, Mainasara ya ce. “Kai dai kana son ka hada wa Zee zafi ka dinga tausaya mata tun daga Nigeria fa ta zo Kasar nan saboda ni, ya dace a jinjina mata ba dole ta mori wahalar tafiyar da ta yi ba Mainasara ya ce, “Kyale ta in ba haka nia yi mata ba ba za ta Kyale ka mu yi magana ba yanzu ba gashi ta tashi ba

Suka yi darya, Najib ya ce, “Mainasara gida zan tafi gobe, Abba ya gano cewa izuwa yanzu ba karatu ne ya zaunar dani a Kasar nan ba, zargin da suke min ya tabbata gara in tafi” Mainasara ya tsuke fuska, ya ce. “Ka yi wa kanka, na gaya maka idan kana biyewa wadannan tsofaffin babu abin da za ka ribata a lokacinka na rayuwa wanda a cikinsa ne za ka more wa rayuwarka ka hole yadda ka so” A wannan lokacin ba zugar da Mainasara bai yi wa Najib ba ya ce, tafiya kawai zai yi, ya yi hakuri shi ma yanzu hankalinsa ya yi gida. Hankalin Mainasara ya tashi matuka, da gaske yana matukar son Najib, ba ya son rabuwarsiu a bisa dole ya Kyale shi Bayan kwana biyu suka nufi gida, Najib yana matukar jin haushin Abdallah, ko magana ba ya son yi masa sosai. Abdallah kam kallonsa yake shi ma ya dauke kansa, tuni ‘yan gidansu sun zo taryar Najib cikin farin ciki. Fati da Buhaila da Ihsan sun ci uban ado da wani farin leshi mai kyan gaske da tsada ya sha dinki mai ban sha awa zai wahala namiji ya yi musu kallo daya ya hakura, Mama ce kawai ba ta zo ba, Abdallah da Najib murmushin

yake kawai yake zuciyarsa ko kadan ba ta farin cikin tahowa gida ya bar ‘yammatansa ną holewa a Malaysia cike da kewa. Su Fati suka tsuguna suka gaida shi, ya amsa daya bayan daya ya zuba idanunsa a kan Buhaila, ya ce. “Buhaila haka ki ka Kara’girma? Kunya ta kamata, ta sunkuyar da kai. Ya jinjina kai ya ce. Tabdijan, ashe lokacin aurenku ya zo”. A rayuwar Najib yana masifar son mace mai nono da duwawu kuma fara, ko ba ta da kyan fuska ba zai damu ba, shi dai in zai kwanta a jikinta ko ina laushi ya yi daidai, sai ya ga Buhaila komai na jikinta ya yi daidai da ra’ayinsa, ba a batun kyan fuska yake tunanin wai shin me wannan yarinyar ta rasa a rayuwarta ta fannin kyau? Tabbas babu. Najib yana wannan tunani ne a kan hanyarsu ta komawa gida, Buhaila na gefensa tana zuba masa hira, muryarta na ratsa sassan jikinsa yadda ka san ya rungume ta. Lokaci guda ya fada cikin ,mawuyacin hali, Buhaila na da kyau na garari, ga iya ado, ba ya son dauke idonsa a kanta.

Nan take ya ji damuwar da yake ciki na dawo wa gida ta fita daga ransa, kallon Buhaila ya haifar da farin ciki da sabon yanayi mai dadi da nishadi a zuciyarsa. Abdallah yana daya motar wadda Ihsan ta jawo yana zaune gefen Ihsan dih ya yi tagumi shi ma hankalinsa na kan Buhaila, kwanakin da ya yi a Malaysia ba awa dayan da za ta wuce bai shiga fargabar kada ya rasa Buhaila ba, da tunanin yadda zai fuskance ta da maganar soyayya, ga soyayyar tata tana ninkuwa a zuciyarsa har an kai matakin da yake jin zai iya rasa ransa a kan Buhaila. Suka iso gida kowa hankalinsa na kan Buhaila, kowanne da abin da zuciyarsa ta ke ayyana masa ita, kowa da yadda ya dauke taa zuciyarsa, Abdallah na matukar son Buhaila a zuciyarsa, amma yana da hakurin jurewa zuciyarsa da abin da yake so zai matuKar dadewa yana son abu ya kasa bayyanawa a takaice dai shi mutum ne mai juriya da zurfin ciki, yayin da Najib ya kasance sha yanzu magani yanzu, ballantana a kan batun soyayya k abin da Najib ke so yanzun nan zai bayyana. Yanzu hakan jira yake ya kebe da Buhaila ya…”

Leave a Reply

Theme by Anders Norén