labaran duniya

Buhari zai kaddamar da yakin neman zabe

A yau ne ake sa ran kaddamar da yakin neman zaben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom.

Tsohon gwamnan jihar ta Akwa Ibom Sanata Godswill Akbabio shi ne shugaban yakin neman zaben na Shugaba Buhari.

Hakan ne ma ya sa ake ganin cewa an zabi jihar ta Akwa ibom ta zama jihar da za’a kaddamar da yakin neman zaben.

Duk da cewa jamiyyar adawa ta PDP ce ke da iko a jihar, Sanata Akpbabio dan siyasa ne mai karfin fada a ji wanda kuma yake da tasiri a harkokin siyasar jihar.

Wannan dai shi ne yakin neman zabe karo na 5 da Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a Najeriya.

A 2003 ya yi yakin neman zabe tare da Chuba Okadibo a matsayin mataimakin sa.

Haka a 2007 ya yi yakin neman zaben tare da Edwin Ume-Ezeoke.

A 2011 ya fito tare da Tunde Bakare a matsayin mataimaki.

A zaben 2015 kuma tare da Farfesa Yemi Osibanjo wanda a lokacin ne ya yi nasarar lashe zaben.

A yanzu, ya kara zabar Farfesa Yemi Osinbanjo a matsayin mataimakinsa domin neman shugabancin kasar karo na biyu.

Mutane da dama suna jira su ga yadda wannan yakin neman zaben na Shugaban Najeriya zai kasance.

Hakan ba ya rasa nasaba da cewa a 2014, akwai jiga-jigan ‘yan jam’iyyar ta Apc da dama wadanda aka zagaya dasu wajen yakin neman zaben amma daga baya sun sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu.

Babban abin tambaya a nan shi ne, ko za’a samu taron mutane kamar yadda aka samu a yakin neman zaben shekarar 2014 koko a’a?

Ana sa ran dai a wannan lokacin shugaban zai ci gaba da yakin neman zaben ne akan samar da tsaro a kasar da kuma yaki da cin hanci da rashawa da kuma kara habaka tattalin arzikin kasar.

A kwanankin baya ne dai gwamnatin jihar ta Akwa Ibom ta fitar da sanarwar cewa ba za ta yarda ayi amfani da filin wasa na jihar ba domin gudanar da yakin neman zaben sakamakon gasar kwallon Firimiya ta Najeriya da za’ayi a fili.

Daga baya ne dai gwamnatin jihar ta amince da ayi amfani ta filin wasan domin kaddamar da yakin nemen zaben.

Leave a Reply

Theme by Anders Norén